NE

News Elementor

Bago: lna Goyon Bayan Wa’adin Mulki Ɗaya Ga Gwamnoni

Gwamnan jihar Niger, Muhammad Umaru Bago, ya jaddada goyon bayansa ga ayyana wa’adin mulki sau daya kacal ga gwamnoni, matakin ya ce zai inganta sha’anin tafiyar da gwamnati.

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi da mataimakansu, da kwamishinoni da wakillan hukumomi a fadar gwamnatin jihar dake birnin Minna.

Bago ya ce ba domin fargabar zaben dake tafe ba, da ya dauki matakai masu tsauri kan wasu jami’an gwamnatinsa, inda ya jaddada cewa idan shugaba ya san wa’adin mulki daya zai yi, to zai gudanar da mulkinsa ba tare da matsin lamba ta yan siyasa ba.

Gwamnan ya ci-gaba da cewa, akwai abubuwa da dama da ya ke son aiwatarwa amma kuma yana tsoron zabe mai zuwa, musamman korar wasu jami’an gwamnatinsa ba su da wani amfani.

A cewarsa, jami’an gwamnatin sun kasa a aikin da aka basu, kuma sun zamewa gwamnatin ala-ka-kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM