NE

News Elementor

Da sana’ar ƙosai mahaifiyata ta rene ni har na girma-Sunday Dare

Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa, Sunday Dare, ya yi tsokaci kan cece-kucen da suka biyo bayan batun sayar da ƙosai, gasa masara da kuma yin ƙuli-ƙuli.

A ranar Juma’a, martani mai zafi ya mamaye kafafen sada zumunta bayan Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta shawarci ‘yan Najeriya da su rungumi ƙananan sana’o’i.

Ta buƙaci ‘yan Najeriya su yi la’akari da sana’o’i irin su suya da sayar da ƙosai, gasawa da sayar da masara, da kuma sarrafa ƙuli-ƙuli, tare da wasu ƙananan sana’o’i.

Cece-kucen ya ƙara ƙamari bayan wani bidiyon jawabin nata ya bazu a kafafen sada zumunta, lamarin da ya jawo suka daga wasu ‘yan Najeriya da suka ce kalaman nata ba su nuna fahimtar irin matsin tattalin arziƙi da wahalhalun da miliyoyin iyalai ke fuskanta ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM