Rahotanni suna nuna cewa daga sansanin sojojin Amurka de ke ƙasar Ghana a Afirka ta Yamma ne Trump ya sa aka ƙaddamar da harin da sojojinsa suka kai a jihar Sokoto.
Kafar PRNigeria ce ta ruwaito hakan daga majiyoyi, inda ta ce Amurka ta yi amfani da makami mai cin dogon zango ne, “a kan ƴan ta’adda da ke arewacin Najeriya.”
Kafar ta ruwaito cewa harin ya biyo musayar bayanan sirri tsakanin Amurka da Ghana da ma ƙasar Najeriya da aka ƙaddamar da harin.
Shugaban Amurka Donald Trump ne ya sanar da cewa sojojin ƙasarsa sun kai hari a arewa maso yammacin Najeriya kan mayaƙan IS.
Gwamnatin Najeriya dai ta ce tana sane da hari, kuma da sahalewarta Amurka ta kai harin.
