Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP), Adewole Adebayo, ya yi alkawarin sanya tsarin samar da wutar lantarki mai aiki da hasken rana mai ƙarfin kilowatt 11 zuwa 15 a kan rufin kowane gida a Najeriya cikin watanni 11 bayan ya kama mulki, idan aka zaɓe shi a shekarar 2027.
Adebayo ya yi wannan alkawarin ne a ranar Talata, yayin da yake amsa tambayoyi a wata hira da gidan talabijin na Arise Television, a cikin shirin ‘Prime Time.’
Ya ce gwamnatinsa za ta kafa masana’antun kera na’urorin hasken rana a sassa daban-daban na ƙasar, tare da horas da ’yan Najeriya kan yadda ake sanyawa da kuma kula da tsarin samar da wutar lantarki ta hasken rana.
Adebayo ya ce a baya ya taba bai wa gwamnati shawarwari kan matsalolin wutar lantarki, sannan ya yi gwaje-gwaje kan fasahar hasken rana a garinsu, inda ya ce ya horas da kusan mutane 2,000.