NE

News Elementor

Dickson ya roƙi Obi, Kwankwaso da sauran ‘yan takara su ci gaba da zama a NDC

Jagoran Jam’iyar NDC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Seriake Dickson, ya yi kira ga ‘yan takarar jam’iyyar, ciki har da ɗan takarar shugaban ƙasa Peter Obi, mataimakinsa Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, da sauran masu neman mukamai, da kada su fice daga jam’iyyar bayan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ta yanke kwanan nan.

Dickson ya bayyana hakan ne a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV a ranar Lahadi, yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa wasu ‘yan takara na tunanin barin jam’iyyar sakamakon hukuncin kotun.

Takaddamar ta samo asali ne bayan hukuncin da Mai Shari’a Isah Dashen na Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ya yanke a ranar Juma’a, inda ya soke hukuncin da kotun ta yanke a ranar 10 ga Disamba, 2025, wanda ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi wa jam’iyyar NDC rajista a matsayin jam’iyyar siyasa.

Mai shari’ar ya bayyana cewa hukuncin da aka yanke a baya ya shafi haƙƙin jam’iyyar Peace Movement Party (PMP), wadda ta yi iƙirarin cewa tambarin da aka yi amfani da shi wajen neman rajistar NDC mallakinta ne, amma ba a shigar da ita cikin ƙarar ba.

Da yake mayar da martani kan fargabar da ake yi cewa wasu ‘yan takara sun damu da hukuncin kotun, Dickson ya yi watsi da wannan hasashe, yana mai tabbatar wa mambobin jam’iyyar cewa NDC na nan daram kuma tana ci gaba da tafiya kan tsarinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM