NE

News Elementor

Dino Melaye ya ce Tinubu da iyalansa su fara tattara kayansu daga Villa gabanin zaɓen 2027

Jagoran jam’iyyar ADC, Dino Melaye, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da iyalansa su fara tattara kayansu daga Fadar Shugaban Ƙasa, yana mai cewa jam’iyyar ADC za ta kayar da APC a zaɓen 2027.

Melaye ya ce yunwa, rashin tsaro, kashe-kashe da matsalolin tattalin arziki sun sa ’yan Najeriya ke ƙara nuna rashin gamsuwa da gwamnatin Tinubu.

Ya kuma zargi gwamnatin da gazawa wajen aiwatar da kasafin kuɗaɗe da kuma biyan wasu kuɗaɗen kwangilolin da aka bayar.

Melaye, wanda ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Arise TV, ya ce sakamakon zaɓen 2027 zai nuna yadda ’yan Najeriya ke son sauyin gwamnati.

Ya kuma zargi Shugaba Tinubu da yin kalaman da ke nuna cewa magudi, tashin hankali da satar ƙuri’u abin yarda ne a siyasa, yana mai cewa hakan bai dace da matsayin shugaban ƙasa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM