NE

News Elementor

Motoci masu sulke sun rage hare-haren yan ta’adda a Sabon Birni ta jihar Sokoto

Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato, Hashimu Dantudu, ya ce tura motocin sulke da gwamnatin jihar ta samar ya taimaka matuƙa wajen rage hare-haren ’yan bindiga a yankin.

Ya ce tun bayan tura motocin, an samu raguwar hare-hare tare da ƙara yawan jami’an tsaro da ake gani a yankin.

Dantudu ya bayyana hakan ne a ƙauyen Tsamaye, yayin ziyarar tawagar gwamnatin jihar da uban jam’iyyar na jihar, Aliyu Wamakko, ya jagoranta domin jajanta wa al’ummar yankin kan rasuwar shugaban APC na ƙaramar hukumar, Amadu Malale.

Shugaban ƙaramar hukumar ya yaba wa Gwamna Ahmed Aliyu bisa samar da motocin, yana mai cewa matakin ya ƙara ƙarfafa yaƙi da ’yan bindiga a jihar.

Ya kuma bayyana fatansa na cewa ci gaba da ƙoƙarin gwamnati wajen inganta tsaro zai taimaka wajen kawo ƙarshen ayyukan ’yan bindiga.

Gwamnatin Jihar Sokoto ta ce ta sayi motocin sulke 62 da babura 2,000, domin raba su ga hukumomin tsaro don ƙarfafa ayyukan yaƙi da ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM