
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage zaman sauraren karar tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i har zuwa ranar 23 ga watan Afrilu domin ya gurfana a gabanta.
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ce ta shigar da ƙara kansa bisa zarge-zarge guda uku ciki har da sauraren wayar mai ba shugaban kasa shawara kan harka tsaro ba bisa ka’ida ba a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channel.
Tun da farko kotu ta sanya ranar 25 ga watan Fabrairu domin gurfanar da tsohon ministan.
Sai dai El-Rufa’i bai halarci zaman kotun na yau Larba ba.