
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya goyi bayan kafa hukumar tsaron gandun daji a Najeriya domin kakkaɓe ƴan bindiga daga dazukan ƙasar nan.
Malamin ya kuma buƙaci sabuwar hukumar da ake shirin kafawa ta yi amfani da ƙarfin tuwo wajen magance miyagun laifuka.
Da yake jawabi a wajen Tafsirin Ramadan a Kaduna, Gumi ya yi gargaɗi kan amfani da hare-haren sama, yana mai cewa hakan na iya jawo asarar rayukan fararen hula.
Ya kuma buga misali da abin da ya faru a Tudun Biri da ke Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, inda aka ruwaito cewa sama da mutum 100 suka mutu sakamakon kuskuren harin jirgin saman rundunar sojin saman Najeriya.