
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da wasu mutum biyar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin ɓoye inda tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Timipre Sylva, yake.
Wadanda ake tuhuma sun haɗa da Reuben Ayuba, Musa Mohammed, Friday Paul, Paganengigha Anagaha da Ayebaifie Suobite.
Ana zarginsu da taimakawa wajen ɓoye Sylva, wanda DSS ta bayyana a matsayin wanda jami’an tsaro ke nema.
Dukkan waɗanda ake tuhumar sun musanta laifukan da ake zarginsu da su. Alƙalin kotun, Peter Lifu, ya ba da belin su kan naira miliyan biyar kowannensu tare da sharuɗɗan gabatar da mutane biyu da za su tsaya musu.
A watan Afrilu ne gwamnatin tarayya ta gurfanar da wasu mutum shida bisa zargin shirya juyin mulki domin hambarar da Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu.
Ko da yake an ambaci sunan Sylva a cikin takardun tuhumar, ba a sanya shi cikin waɗanda ake tuhuma ba, sai dai an zarge shi da haɗa baki da sauran mutanen da ake zargi.