Babban Daraktan Hukumar DSS, Oluwatosin Ajayi, ya ce hukumar ta kama muggan makamai 676 da harsasai 332,874 tsakanin ranar 29 ga Mayu da watan Agustan wannan shekara.
Ajayi ya bayyana cewa hukumar ta kuma samu nasarar gurfanar da masu aikata laifukan ta’addanci, inda aka yanke wa mutum bakwai hukuncin kisa. Ya ce mutum hudu daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin kisan suna Owo, yayin da mutum daya-daya suka fito daga jihohin Kogi, Katsina da Sokoto.
Ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda aka samu da laifuka daban-daban an yanke musu hukuncin daurin shekaru 20 zuwa 40 a gidan yari.
Daraktan ya yi kira da a kara tsaurara dokokin Najeriya, musamman wajen hukunta masu aikata ta’addanci, yana mai cewa samar da bayanan sirri kadai ba zai wadatar wajen kawo karshen ta’addanci da sauran manyan laifuka ba.
Ajayi, wanda ya bayyana hakan yayin ganawa da manyan editoci domin bikin cikar sa shekaru biyu yana jagorantar DSS, ya kuma bukaci a daina kallon matsalar ta’addanci ta fuskar kabila ko siyasa.
Ya ce ya kamata a hukunta duk wani dan ta’adda bisa tanadin doka, ba tare da la’akari da kabilarsa ko addininsa ba.
Ya ce cikin shekaru biyu da suka gabata, DSS ta samu nasarori da dama ta hanyar inganta hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, gurfanar da masu laifi, mutunta hakkin dan Adam da kuma aiwatar da sauye-sauye a cikin hukumar.