Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta gurfanar da mutane huɗu ciki har da ƴan ƙasar Indiya uku da wani ɗan Najeriya a gaban Babbar Kotun Jihar Kwara da ke Ilorin, a ranar Laraba 17 ga Disamba, 2025.
Ana zargin mutanen da aikata laifuka biyu da suka shafi haɗin baki da kuma zamba cikin aminci, laifukan da EFCC ta ce sun faru ne a lokacin da suke aiki a Kamfanin KAM Steel, tsakanin Nuwambar 2024 zuwa Satumba 2025.
Hukumar EFCC ta bayyana wannan batu ne ta hanyar shafinta na X (Twitter).
Lokacin da aka karanta musu ƙarar a gaban kotu, dukkan waɗanda ake tuhuma sun musanta zarge-zargen da ake yi musu.
Lauyan EFCC, Cosmas Ugwu, ya roƙi kotu da ta bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a fara shari’a.
Sai dai lauyoyin kariya sun nemi a ba wa waɗanda ake tuhuma beli, suna mai cewa laifukan da ake zargin su da su na daga cikin laifukan da doka ta amince a ba da beli a kansu.
A nasa bangaren, lauyan EFCC ya jaddada cewa wasu daga cikin mutanen ba ‘yan Najeriya ba ne, don haka akwai yiwuwar su tsere idan aka sake su, inda ya kuma buƙaci kotu ta hanzarta gudanar da shari’ar.
Bayan sauraron ƙorafe-ƙorafe da hujjojin bangarorin biyu, Alkalin kotun, Sulaiman Akanbi, ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar Juma’a 19 ga Disamba, 2025.