Ramadana wata ne mai alfarma da Musulmai ke shafe tsawon watan suna ibadar azumi, ɗaya cikin shikashikan Musulunci.
Wata ne da ake son Musulmi ya siffantu da bautar Allah da addu’o’i tare da neman gafara ga mahalicci, kamar yadda malamai ke bayyanawa.
Watan Ramadan baki ɗayansa na ƙunshe da falala tun daga 10 na farko, zuwa 10 na tsakiya, da kuma kwanaki mafi daraja na 10 ta ƙarshe.
Shiekh Abubakar Baban Gwale ya yi wa BBC bayani kan falalar 10 ta tsakiya da kuma abubuwan da ake son Musulmi ya himmatu da su.
Malamin ya ce Ramadan wata ne da ake ƙara alherin mumuni a cikinsa – duk lokacin da aka ƙara kwanaki alherinsa yana kara ƙaruwa.
“Manzon Allah (SAW) ya ce farkon watan Ramadan rahama ne, tsakiyarsa kuma gafara ce ƙarshensa kuma ‘yanta mutum ne daga wuta,” in ji Baban Gwale.
Shehin malamin ya ce idan aka shiga zango na gafara ba wai ana goge rahama ba ne – ana son mutum ya ninka ibada domin ya haɗa rahama da kuma gafara tare da kara kusanci ga Allah.
Cigaban kwanakin Ramadan ƙarin samun falala ne da kuma kusantar dare mai albarka na Laylatul Kadari.