Sama da mutum 20,000 ne ke zauna jarabawar gwaji ta kwamfuta ta Rundunar Sojin Saman Najeriya da ake gunarwa a yankuna kasar nan, domin shiga shirin daukar ma’aikata yan kwas 46 na shekarar 2025.
Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin saman Nigerai, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar Lahadi, ta ce an rarraba cibiyoyin gwajin a fadin kasar nan ne domin tabbatar da cewa an ba kowa damar zauna jarabawar da kuma tsarin daukar aiki na gaskiya da cancanta.
Da yake magantawa a kan shirin, Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya ce tsarin daukar aikin yana gudana ne bisa adalci, gaskiya, da bin ka’idojin da aka shata.
Ya ce jarawabawar gwajin wani mataki ne mai muhimmanci wajen zaben wadanda suka cancanta, inda ya kara da cewa nagartattun jami’ai su ne ginshikin karfin aikin rundunar.
Ana gudanar da jarabawar gwajin nea cibiyoyi 15 da aka ware a fadin kasar nan, ciki har da Sokoto, Minna, Kaduna, Kano, Bauchi, Maiduguri, Yola, Makurdi, Jos, Ilorin, Ipetu-Ijesa, Enugu, Benin, Port Harcourt da Ikeja.