NE

News Elementor

FRSC ta tabbatar da mutuwar ɗaliban jami’ar Jos 8 a haɗarin mota

Hukumar kiyaye haɗurra ta Najeriya, FRSC a jihar Filato ta tabbatar da mutuwar daliban jami’ar Jos takwas sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da su.

Hadarin dai ya auku ne da misalin karfe biyu na dare a akan titin zuwa Zaria a birnin Jos inda wasu da dama suka jikkata.

FRSC ta ce hadarin ya faru ne yayin da motar da ɗaliban ke ciki ta yi taho mu gama da wata motar kaya, lamarin da ya janyo mummunan lahani.

Rahotanni sun ce ɗaliban na kan hanyarsu ta komawa ɗakunan kwanansu bayan fitowa daga shaƙatawar dare lokacin da abin ya faru.

Ana dai cigaba da kula da wasu ɗalibai biyu da suka tsira daga hatsarin bayan an garzaya da su zuwa wani asibiti mafi kusa domin samun kulawar gaggawa.

Daga karshe hakumar FRSC ta ce an fara bincike don gano ainihin musabbabin faruwar wannan mummunan haɗari, tare da kira ga direbobi da su rika tuki cikin natsuwa musamman a lokutan dare domin guje wa irin haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM