Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi domin kawo ƙarshen ’yan bindiga da sauran laifukan da ke addabar wasu sassan ƙasar.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a cikin saƙonsa na ranar samun ’yancin kan Najeriya, yayin da ƙasar ke bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai a yau Alhamis. Ya yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa tallafin da take bai wa jihar Sokoto wajen yaƙi da ’yan bindiga, yana mai cewa ya kamata a ci gaba da wannan haɗin gwiwa domin samun zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa.
Aliyu ya ce gwamnatinsa ta samar da kayan aiki domin ƙarfafa ayyukan hukumomin tsaro na yau da kullum, ciki har da motoci sama da 200 na sintiri, motocin yaƙi masu sulke na Buffalo guda 100, babura 200, kayan aikin tsaro 3,200, rigunan kariya daga harsasai 2,000 da na’urorin hangen dare guda 200.
Ya kuma ce gwamnati ta samar ta inganta na’urar bibiyar DSS daga fasahar 4G zuwa 5G domin ƙarfafa sa ido da tattara bayanan sirri. Haka kuma, gwamnatin ta kafa Sokoto State Community Guard Corps, tare da samar masa da motoci kirar Hilux guda 40 da babura 700.
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta taimaka wajen kafa sansanin sojoji a Illela da kuma sansanin ’yan sandan Mobile Police a ƙauyen Tara da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni. Matakan sun zo ne a cikin jerin matakan da gwamnatin ke ɗauka domin ƙarfafa ayyukan tsaro a jihar.
Ahmed Aliyu ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa na da ƙudirin kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga a Sokoto, tare da roƙon jama’a da su mara wa ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da tsaro. musamman ta hanyar haɗa kai da hukumomin tsaro.
A ƙarshe, gwamnan ya tuna da waɗanda suka kafa Najeriya, inda ya yi kira ga ’yan ƙasa da su koyi darasi daga sadaukarwarsu da kishin ƙasa wajen gina Najeriya mafi inganci.