Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya ce zai yi murabus idan gwamnatin jam’iyyar ba ta fara kawo sauyi a Najeriya cikin shekara guda bayan hawanta mulki ba.
Amaechi ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na AIT ranar Laraba, inda ya ce gwamnati za ta fi mayar da hankali kan tsaro, ilimi da tattalin arziki, tare da yaƙi da cin hanci da rashawa.
Ya ce ba ya nufin za a warware dukkan matsalolin Najeriya cikin shekara guda ba, amma ya kamata ’yan ƙasa su fara ganin alamun sauyi da samun sauƙin rayuwa.
Amaechi ya kuma soki cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi, yana mai cewa matakin bai kawo ingantuwar rayuwa ga talakawa ba.
Ya ƙara da cewa kuɗaɗen da ya kamata a yi amfani da su wajen ci gaban ƙasa na karkacewa sakamakon cin hanci da rashawa.
A cewarsa, idan ADC ta samu nasara a zaɓen 2027, za ta aiwatar da manufofin da za su sauya rayuwar ’yan Najeriya.