NE

News Elementor

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani.

Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata, 3 ga Nuwamba, 2026, da ƙarfe 10:00 na safe.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar a ranar Litinin, ya ce Majalisar ta karɓi wasiƙar buƙatar tantancewar ne daga Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya ƙara da cewa za a gudanar da aikin tantancewar ne bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya.

Sanarwar ta ce za a gudanar da aikin tantancewar ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore.

Sanusi Bature Dawakin Tofa dai shi ne mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, kuma yana cikin mutum biyu da gwamnan ya miƙa sunayensu domin zama kwamishinoni a gwamnatin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM