NE

News Elementor

Gwamnan Kano ya jinjinawa Ɗariƙar Tijjaniyya bisa shirya addu’o’i na musamman domin neman zaman lafiya da haɗin kan ƙasa

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa Ɗariƙar Tijjaniyya ta kasa bisa shirya addu’o’i na musamman domin neman zaman lafiya, haɗin kai da bunƙasar tattalin arzikin Najeriya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa labaran Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan kammala taron Zikirin Tijjaniyya na shekara-shekara da addu’o’i na musamman ga Najeriya, wanda aka gudanar a fadar mai martaba Sarkin Kano.

Lokacin da yake jawabi ga dubban mahalarta taron, Gwamna Abba ya ce addu’ar ta zo a kan lokaci, yana mai jaddada cewa shugabanni na buƙatar shiriyar Allah domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da aiwatar da ayyukan ci gaba.

Ya kuma bayyana cewa ya sanar da shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, game da taron addu’ar, inda shugaban ƙasar ya nuna farin cikinsa da wannan shiri, sai dai ya ce bai samu damar halarta ba saboda wani muhimmin aiki na gaggawa.

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da tallafa wa irin waɗannan tarukan addini da ke inganta zaman lafiya da haɗin kan al’umma.

Haka kuma ya yaba wa iyalan Sheikh Ibrahim Nyass da suka fito daga ƙasar Senegal domin halartar taron, tare da sauran manyan malaman addini daga sassa daban-daban na Najeriya.

A nasa jawabin, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, ya tabbatar da ci gaba da goyon bayan Ɗariƙar Tijjaniyya ga gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana mai cewa mambobin ɗariƙar sun fara yi masa addu’a tun daga shekarar 2022 kuma za su ci gaba da hakan.

An shafe sama da sa’o’i shida ana gudanar da taron kafin a kammala da addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM