NE

News Elementor

Gwamnatin jihar Sokoto ta musanta sace ɗalibai 18 na kwalejin lafiya ta Gamji

Gwamnatin Jihar Sokoto ta musanta rahoton yin garkuwa da ɗalibai 18 na Kwalejin Lafiya ta Gamji College da ke Sokoto yayin da suke tafiya zuwa Jihar Oyo.

Wannan na cikin sanarwar da Daraktan yaɗa labaran gidan Gwamnatin jihar, Abubakar Bawa, ya fitar a ranar 5 ga Oktobar 2026.

Gwamnatin ta ce babu wani ɗalibi na Gamji College of Health Technology da aka yi garkuwa da shi, tana mai buƙatar jama’a su yi watsi da rahoton da ta bayyana a matsayin wanda ba shi da tushe.

Sanarwar ta fayyace cewa wadda aka ruwaito an yi garkuwa da ita, ita ce Halima Sokeni, tsohuwar ɗalibar Gamji College of Nursing Sciences da ke More Area, Sokoto, wadda ta kammala karatun ungozoma a watan Satumbar 2026.

Gwamnatin ta ce an, yi garkuwa da ita ne tare da wasu fasinjoji a Jihar Neja yayin da take komawa gida a ranar 1 ga Oktobar, 2026.

Gwamnatin Sokoto ta buƙaci ’yan jarida da kafafen yaɗa labarai su dinga tabbatar da bayanai kafin wallafa wa domin kauce wa yaɗa bayanan ƙarya ko masu tayar da hankalin jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM