Jirgin rundunar sojin saman Nigeria ya yi hatsari a yankin Igbokoda a jihar Ondo, dauke da mutum 32.
Wani jagora a yankin ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce har yanzu ba a san ainihin inda jirgin ya fadi ba da kuma sauran bayanan da za su biyo baya.
Tuni rundunar sojin saman Nigeria ta kaddamar da aikin ceto da bincike bayan faduwar jirhin na ATR-42.
Bayanai sun ce jirgin na kan hanyarsa ta sintire daga Benin zuwa Legas, lokacin da lamarin ya faru.
A wani bayani da directan yada labarai na rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar, rundunar ta tabbatar da kudurinta wajan ceto mutanen da ke cikin jirgin.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, ministan sufurin sama, Festus Keyamo, ya ce mutanen da ke cikin jirgin sun kunshi fasinjoji 25 da matukansa su 7.