Gwamnatin Jihar Sokoto ta bayar da gudummawar naira miliyan 38.25 da hatsi ga iyalan sojoji 24 da suka mutu da kuma sojoji 57 da suka jikkata, domin nuna jinjinawa bisa sadaukarwar da suka yi wajen yi wa ƙasa hidima.
Gudummawar, wadda Sakataren Gwamnatin Jihar, Bello Sifawa, ya gabatar a madadin gwamnatin jihar, ta haɗa da shinkafa, masara da gero ga waɗanda za su amfana.
Da yake magana, Sifawa ya ce sadaukarwar da sojojin suka yi wajen kare rayuka, tabbatar da zaman lafiya da kuma kare cikakken ikon ƙasar nan ya cancanci a yaba musu tare da nuna godiya.
Sakataren Gwamnatin Jihar ya bayyana cewa wannan gudummawa ta nuna goyon bayan gwamnatin jihar ga rundunar soji da kuma ƙudurinta na tallafa wa jami’an da ke jefa rayukansu cikin haɗari yayin gudanar da ayyukansu, da kuma iyalan waɗanda suka mutu suna bakin aiki.
Ya isar da ta’aziyyar gwamnati ga iyalan sojojin da suka rasu, tare da yi wa sojojin da suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa.
Ya kuma tabbatar musu da cewa ba za a manta da sadaukarwar da suka yi ba.