Gwamnatin Jihar Sokoto ta dauki matakin tallafa wa wani maraya mai shekaru 16, Muhammad Sirajo Abubakar, wanda ya samu maki 353 a jarabawar share fagen shiga jami’a ta UTME ta shekarar 2026.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, Ibrahim Iya, ya fitar a ranar Laraba, matakin ya biyo bayan kwazon da Muhammad ya nuna a jarabawar da kuma yadda labarin ya ja hankalin jama’a.
Muhammad, wanda ya rasa iyayensa biyu tun yana karami, ya samu maki 92 a Lissafi, 67 a Turanci, 98 a Physics da 96 a Chemistry a jarabawar JAMB ta shekarar 2026.
Sakamakon jarabawarsa ta WAEC ya kuma nuna cewa ya samu A uku, B hudu da C daya, yayin da har yanzu ake jiran sakamakon Biology.
Dalibin yana neman gurbin karatun Injiniyan Mechatronics a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
A cewar sanarwar, Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, Farfesa Isa Muhammad Maishanu, ya tuntubi Mai Kula da JAMB na jihar, Ibrahim Muazu Hassan, bayan da ya ci karo da labarin Muhammad a kafafen sada zumunta.Kwamishinan ya umarci jami’in da ya tuntubi dalibin tare da shirya yadda zai je ma’aikatar domin duba yiwuwar tallafa masa.
Daga bisani, an kai Muhammad Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi a ranar Talata, inda kwamishinan da jami’an ma’aikatar suka tarbe shi.