Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yaye ‘yan matan Chibok 18 da aka ceto daga hannun ‘yan ta’adda bayan kammala horas da su kan sana’o’i daban-daban, tare da ba kowacce tallafin fara kasuwanci na naira miliyan ɗaya da kayan aiki.
Ministar harkokin mata da ci gaban al’umma, Imaan Suleiman-Ibrahim, ta bayyana hakan a wani bikin yaye daliban da aka gudanar a Yola, inda ta ce 14 daga cikinsu sun kware a fannin ɗinki, yayin da huɗu suka samu horo a harkar girke-girke.
Ta ce za a kuma bai wa rukuni na biyu da ya ƙunshi ‘yan matan Chibok 33 tallafin naira miliyan ɗaya kowacce bayan sun kammala horonsu. Haka kuma, ‘yan mata 12 da ke shirin kammala karatu a Jami’ar American University of Nigeria (AUN) a shekarar 2026, da wasu 21 da za su kammala a 2027, su ma za su samu irin wannan tallafi.
Ministar ta ƙara da cewa iyayen dukkan ‘yan matan Chibok 221 za su karɓi tallafin naira 200,000 kowannensu tare da kayan aikin dogaro da kai domin inganta rayuwarsu.
Ta kuma ƙarfafa gwiwar ‘yan matan da kada su bari abin da ya faru da su shekaru 12 da suka gabata ya zama abin da zai ayyana rayuwarsu, tana mai cewa ya kamata duniya ta riƙa saninsu saboda nasarori da gudummawar da suke bayarwa.
A nasa jawabin, shugaban kamfanin ba da shawarwari na Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, Farfesa Ibrahim Danjuma, ya taya waɗanda suka kammala horon murna, tare da bayyana fatan cewa za su zama fitattun ‘yan kasuwa masu dogaro da kai a nan gaba.