Gwamnatin Tarayya ta ta hannun hukumar kula da jami’oi ta kasa (NUC), ta bai wa Iconic Open University cikakken lasisin gudanar da jami’ar mai zaman kanta a Najeriya.
An bayar da lasisin ne a ranar Talata 22 ga Satumba 2026, a Abuja, lamarin da ya mayar da jami’ar cikakkiyar jami’a mai zaman kanta wadda aka amince da ita a hukumance.
Wannan mataki ya kawo ƙarshen wa’adin lasisin wucin gadi da jami’ar ta fara da shi tun a shekarar 2023, bayan da ta kammala aikin tantancewa na tsawon wa’adin gwaji.
A watan Mayun 2026, hukumar NUC ta gudanar da cikakken bincike da tantance tsarin karatu da shirye-shiryen jami’ar da malamai da tsarin gudanarwa da ababen more rayuwa da tsarin tabbatar da ingancin ilimi da kuma sauran muhimman sassa na jami’ar.
Bayan kammala wannan tantancewa, hukumomin da ke kula da jami’o’in Najeriya sun amince da ci gaban da Iconic Open University ta samu tare da bai wa jami’ar cikakken lasisin gudanarwa.
An bayar da lasisin ne tare da sa hannun Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da hukumar kuka da jami’oi NUC, ƙarƙashin jagorancin Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, da Babban Sakataren hukumar NUC, Farfesa. Abdullahi Yusufu Ribadu.
Da wannan lasisi, Iconic University ta samu cikakkiyar damar ci gaba da gudanar da karatun jami’a da bayar da digiri bisa tanade-tanaden dokokin Najeriya da ka’idojin hukumomin da suka dace.
Samun cikakken lasisin bayan shekaru uku kacal da fara aiki a shekarar 2023 na zuwa ne a daidai lokacin da jami’ar ke ƙara faɗaɗa shirye-shiryenta na samar da damar samun ingantaccen ilimi ga al’umma.
Hukumar gudanarwar Iconic University ta bayyana godiyarta ga Gwamnatin Tarayya da hukumar kula da jami’oi NUC da ma’aikata, malamai, ɗalibai, abokan hulɗa da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudunmawar da suka bayar wajen cimma wannan mataki.