Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya ce Gwamnatin Tarayya ta ƙuduri aniyar kawo ƙarshen ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga a ƙasar nan fiye da kowane lokaci.
Akume ya bayyana hakan ne a wajen taron bayar da lambar yabo kan Zaman Lafiya da Tsaro da aka gudanar a Abuja.
Wanda ya wakilce shi, Babban Sakataren Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Aminu Yar’Gaya, ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su mara wa gwamnati baya ta hanyar yin sahihin rahoto mai adalci da daidaito.
Ya kuma jaddada muhimmancin kafafen yaɗa labarai tare da kira a gare su da su ci gaba da taimakawa rundunar soji da sauran masu ruwa da tsaki a yaƙi da matsalar rashin tsaro