NE

News Elementor

Gwamnatin tarayya ta hana ministoci da manyan jami’an gwamnati yin balaguro ƙasashen waje ba tare da neman izini ba

Gwamnatin tarayya ta haramtawa ministoci, shugabannin ma’aikatu da hukumomi da sauran manyan jami’an gwamnati, yin balaguro zuwa kasashen waje ba tare da samun izini daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya ba.

Gwamnatin ta kuma umarci ma’aikatar harkokin waje ta tabbatar duk jami’in da za iyi balaguro zuwa kasashen waje ya gabatar da takardar izini daga sakataren gwamnatin tarayya kafin a fara shirye-shiryen bashi visa.

Umarnin na kunshe a wata takarda mai dauke da sa-hannun sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, wacce aka aikewa manyan jami’an gwamnati da shugabannin hukumomi.

Matakin na zuwa ne daidai lokacin da ake sa-ido kan hukumomi da manyan jami’an gwamnati wadanda ke wakiltar gwamnatin tarayya, bayan badakalar Prince Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da kafa hukumar bogi.

Tuni batun ya haifar da rudani kan yadda wasu daidaikun mutane ke ikirarin cewa su jami’an gwamnati kuma har su yi balaguro zuwa kasashen waje da sunan wakiltar Nigeria ba tare da samun izini ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM