Gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam’iyyar APC sun nisanta kansu daga duk wani ƙawance ko yarjejeniya ta siyasa da wani mutum ko jam’iyyar adawa gabanin babban zaɓen 2027, suna mai jaddada cewa za su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga APC da tsarin siyasarta.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban kungiyar gwamnonin APC, kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya bayyana hakan ne a ƙarshen taron gwamnonin jam’iyyar da aka gudanar a Abuja a daren Litinin.
Uzodimma ya ce gwamnonin APC ba su kulla wata yarjejeniya a hukumance da wani mutum ko wata jam’iyyar adawa ba dangane da zaɓen shekarar 2027.
Wannan matsaya ta zo ne a daidai lokacin da ministan birnin tarayyar Nijeriya Abuja, kuma jagoran jam’iyyar PDP na ƙasa, Nyesom Wike, ke jagorantar wani yunƙurin kafa ƙungiyar siyasa mai suna Rainbow Coalition a jihar Rivers.
Wike, wanda ke aiki a gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin APC, ya kasance yana nuna goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sake tsayawa takara da kuma samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Sai dai Wike ya taɓa bayyana cewa gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, da gwamna Hope Uzodimma na da hannu wajen fuskantar wasu ƙalubalen siyasar da yake ciki.
Ministan ya danganta hakan da yadda, a cewarsa, ƙungiyar da yake jagoranta ke ƙara yaɗa tasirinsa a faɗin ƙasar, musamman wajen samar da wata kafa ga ’yan siyasar da ke son kalubalantar ’yan takarar APC a zaɓen gwamna da na majalisar dattawa.
Sai dai a wani yanayi da ake kallon a matsayin martani ga irin waɗannan matakai, gwamnonin APC sun bayyana cewa ba za su goyi bayan wani tsarin siyasa da zai iya haifar da rikici, rarrabuwar kai ko kuma biyayya ga wasu muradun da suka saba da na jam’iyyar ba.
Uzodimma, wanda ya karanta sanarwar matsayar gwamnonin bayan taron, ya ce babban abin da kungiyar gwamnonin APC ta mayar da hankali a kai shi ne tabbatar da nasarar ’yan takarar jam’iyyar a dukkan matakan zaɓe.
Ya ce gwamnonin sun amince baki ɗaya cewa ba za su shiga ko su goyi bayan wani ƙawance ko tsarin siyasa da zai iya raunana APC, kawo cikas ga sake zaɓen shugaba Tinubu ko kuma cutar da ’yan takarar jam’iyyar a kowane mataki ba.
A cewar Uzodimma, jam’iyyar APC ce ta tsayar da ’yan takarar da za su fafata a zaɓen, don haka gwamnonin za su mayar da hankali wajen ganin sun samu cikakken goyon bayan jam’iyyar.
Ya ce: “kungiyar gwamnonin APC ba ta da niyyar goyon bayan wani ɗan takara a kowane mataki da ba ɗan takarar APC ba ne, saboda ’yan takarar da za su fafata a zaɓen jam’iyyarmu ce ta ɗauki nauyin tsayar da su.”
Gwamnan ya ƙara da cewa tsarin yaƙin neman zaɓen gwamnonin zai kasance ne kawai kan dukkan ’yan takarar APC, daga matakin ƙasa zuwa na jihohi da sauran matakan zaɓe.
Ya ce dukkan ɓangarorin tsarin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar za su yi aiki ne bisa manufofin Shugaba Tinubu da kuma manyan manufofin siyasar APC.
Matsayar gwamnonin ta kuma bayyana irin muhimmancin da jam’iyyar ke bai wa haɗin kan tsarin siyasarta yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
A cewar gwamnonin, ba za su goyi bayan wani tsari da zai haifar da rabuwar kai ko kuma rikitar da tsarin zaɓen jam’iyyar a matakin ƙasa da jihohi ba.
Wannan matsaya na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa das ƙungiyoyin da ke neman tasiri a zaɓen 2027 ke ƙara faɗaɗa tuntuba da neman haɗa kan ’yan siyasa a sassa daban-daban na Nijeriya.
Haka kuma, al’amuran siyasa a gabanin zaɓen 2027 na ƙara ɗaukar zafi, musamman yayin da manyan ’yan siyasa ke ƙulla sabbin alaƙa da dabarun da za su taimaka musu wajen samun rinjaye a zaɓen.
Sai dai gwamnonin APC sun bayyana a sarari cewa matsayinsu shi ne su tsaya kan jam’iyyarsu da ’yan takarar da APC ta amince da su, ba tare da shiga wata yarjejeniya da za ta iya kawo wa jam’iyyar cikas ba.