NE

News Elementor

Hukumar NDLEA ta kama miyagun kwayoyi na Naira Biliyan 3.4

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta ce ta kwace miyagun kwayoyi da darajarsu ta haura N3.4 biliyan, tare da kama wasu mutane a wasu jihohi da Abuja.

Hukumar ta ce ta kwace fiye da kwayoyin Tramadol da opioids miliyan 1.3, da kuma kusan kilogram 6,000 na tabar wiwi.

A tashar Tin-Can Island da ke Legas, NDLEA ta kwace buhunan Canadian Loud 1,200, masu nauyin kilogram 603.75 da darajarsu ta kai N1.81 biliyan.

A Delta, an kama wani mutum mai suna Innocent Ekpe, mai shekaru 49, bisa zargin yin sojan gona a matsayin babban dan sanda domin kauce wa binciken jami’ai. An kama shi dauke da kilogram 292.48 na tabar wiwi, yayin da wani abokin huldarsa shi ma aka kama.

A Edo kuma, NDLEA ta kama wani makanike, Matthew Ossai, mai shekaru 45, inda aka ce an samu kilogram 48 na Canadian Loud da gram 152 na methamphetamine a wajen gyaran motarsa.

Hukumar ta kuma ce ta kama wasu mutane tare da kwace fiye da kwayoyin Tramadol miliyan 1.1 a hanyar Abaji zuwa Abuja, yayin da aka kama wasu da tabar wiwi da sauran miyagun kwayoyi a Legas, Gombe, Imo da Ondo.

A jihar Ondo, jami’an hukumar sun lalata gonar tabar wiwi mai fadin hekta biyu, tare da kama mutane hudu.

Shugaban NDLEA, Brig.-Gen. Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya yaba wa jami’an hukumar tare da umartar su da su ci gaba da gudanar da ayyukan yaki da miyagun kwayoyi bisa bayanan sirri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM