NE

News Elementor

Hukumar NDLEA ta kama wata tsohuwa mai shekara 101, da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a jihar Ogun

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, sun kama wata tsohuwa mai shekara 101, Esther Ogunmabo, bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi a jihar Ogun.

An kama Ogunmabo a garin Ilisan, inda jami’an hukumar suka same ta da buhunan ƙwayar skunk, wani nau’in tabar wiwi, mai nauyin gram 90, wadda ta ce tana sayar wa mazauna yankin.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya ce matar ta shaida wa jami’an cewa ta fara safarar ƙwayoyin ne bayan gobara ta kone shagon kayan masarufinta.

Ya ce ɗaya daga cikin ’ya’yan matar da ke zaune a Legas ce ke shirya kawo mata ƙwayoyin duk bayan kwanaki huɗu, sannan ita kuma ta riƙa sayar da su kaɗan-kaɗan.

Babafemi ya ce Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, ya bayar da umarnin a bayar da belin matar tare da sanya ta cikin shirin ba da shawara saboda tsufanta, yayin da aka kama ’yarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM