NE

News Elementor

Hukumar Yaki Da Shan Miyagun Kwayoyi Ta (NDLEA) Tace Ta Samu Nasarar Kama Mutum 77,792, Da Kwace Miyagun Kwayoyi Kilo 14,847 A Cikin Shekaru 5

Shugaban hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya, Birgediya Janar Buba Marwa ya ce hukumar ta kama masu safarar ƙaya 77,792 tare da ƙace kilogiram na miyagun ƙwayoyi har 14,847 a cikin shekara biyar da suka wuce.

Marwa ya bayyana haka ne a ranar Talata a Abuja a bikin bayar da kyaututtuka da yabo na hukumar NDLEA, wanda aka shirya don girmama manyan kwamandoji da ma’aikatan hukumar bisa ga aikin da suka yi a shekarar da ta gabata.

Ya ce ƙwace miyagun kwayoyi ya kawo cikas ga harkokin safarar miyagun kwayoyi na cikin gida da na kasashen waje, yana mai jaddada cewa nasarorin da aka samu sun nuna cewa Nijeriya ba ta zama mafaka ga ko cibiyar miyagun kwayoyi ba.

A cewarsa, hukumar ta kuma kama wasu masu safarar miyagun kwayoyi guda 128 wadanda aka gano suna taka muhimmiyar rawa a manyan ayyukan safarar miyagun kwayoyi a fadin kasar, inda ta kara da cewa nasarorin sun samo asali ne daga gyare-gyare da aka yi niyya don sake tsara NDLEA don samar da ingantaccen aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM