Mahukuntan Jami’ar Confluence University of Science and Technology (CUSTECH) da ke Osara a jihar Kogi sun kori dalibai biyu bisa zargin aikata luwadi.
Haka kuma, jami’ar ta dakatar da wasu dalibai hudu daga karatu saboda zargin yin fada a harabar makarantar.
Sanarwar da jami’ar ta fitar ta ce majalisar gudanarwar Jami’ar ce ta amince da hukuncin bayan karɓar shawarwarin kwamitin ladabtar da dalibai, bisa tanade-tanaden kundin dokokin ɗalibai da aka sabunta a shekarar 2025.
Mahukuntan jami’ar sun jaddada aniyarsu ta tabbatar da da’a da zaman lafiya a harabar makarantar, tare da gargadin cewa za su ci gaba da hukunta duk ɗalibin da ya karya dokokin jami’ar.