Jam’iyyar ADC ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sake duba amfani da malaman jami’a masu ra’ayin siyasa a matsayin jami’an tattara wa da hada sakamakon zabe a 2027.
Kiran ya biyo bayan rahoton cewa sama da manyan malaman jami’o’in gwamnati 600 daga Arewacin Najeriya sun nuna goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.
A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta ce duk da ’yancin malaman jami’a na goyon bayan dan takarar da suke so, bai kamata a ba wanda ya bayyana bangaren da yake goyon baya aikin tantancewa da bayyana sakamakon zaben da dan takarar ke ciki ba.
ADC ta bukaci INEC ta kafa ka’idojin da za su hana mutanen da suka fito fili suka goyi bayan ’yan takara ko suka shiga harkokin siyasa zama jami’an zabe.
Haka kuma, ta nemi INEC ta wallafa sunayen jami’an tattara sakamakon da za a nada tun kafin zabe, domin jam’iyyun siyasa da jama’a su samu damar nuna duk wani rikici na moriya.