NE

News Elementor

Jam’iyyar Apc A Jihar Zamfara Ta Musanta Batun Komawar Gwamna Dauda Lawal

Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta musanta rahotannin da ke cewa Gwamna Dauda Lawal ya gabatar mata da wata takarda da ke nuna aniyarsa ta komawa cikin am’iyyar.

Jam’iyyar APC ta reshen jihar Zamfara ta bayyana rahoton a matsayin kirkiren labari, a cikin wata sanarwa da ta fitar a daren Juma’a, Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar ta APC a jihar, Mallam Yusuf Idris, ya ce batun mika takardar ya fito daga wani mai amfani da kafafen sada zumunta ba daga majiya mai tushe ba.

Idris ya bayyana rahoton a matsayin wanda ba shi da tushe, ya kuma gargadi wadanda ke yada labaran karya da gangan domin kawar da hankalin jama’a da kuma haifar da tashin hankali mara amfani a cikin jam’iyyar da su daina kokuma su fuskanci hukunci.

Ya jaddada cewa jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara bata karbi wata takarda a hukumance daga Gwamnan Dauda Lawal ko wani jami’in gwamnati ba, hakazalika zuwa yanzu Babu wata alama dake juna cewa Gwamnan zai bar jam’iyya Mai mulkin jihar ta PDP zuwa APC ba.

Mai magana da yawun jam’iyyar ya bukaci ‘yan APC da sauran jama’a, musamman mazauna Jihar Zamfara, da su yi watsi da rahoton gaba ɗaya, yana mai bayyana shi a matsayin wani abu da aka shirya don haifar da rudani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM