NE

News Elementor

Jam’iyyar PDP ta rushe shugabanninta a Kano

Jam’iyyar PDP ta rushe shugabancin jam’iyyar na Jihar Kano, tare da sauke shugaban jam’iyyar na jihar, Dr Bello Gambo Bichi.

Shugabancin jam’iyyar ne ya ɗauki matakin, wanda ya fara aiki nan take, kamar yadda wata wasiƙa mai kwanan wata 24 ga Satumba 2026 ta bayyana.

Jam’iyyar ta ce rushewar ta shafi shugabancin jihar ne kawai, yayin da kwamitocin jam’iyyar na ƙananan hukumomi da mazabu ba su cikin matakin.

PDP ta kuma umarci Kwamitin Rikon Kwarya na Arewa maso Yamma da ya kula da harkokin PDP a Kano har sai an zaɓi sabon Kwamitin Ayyuka na Jihar.

Da yake magana kan matakin, Bichi ya ce ya amince da rushewar a matsayin sadaukarwa domin sulhunta ‘yan jam’iyyar da ƙarfafa PDP a Kano.

Ya ce matakin na daga cikin sharuɗɗan sulhun da aka cimma, musamman bayan sauya tsohon ɗan takarar gwamnan PDP, Dalhatu, da Muhammad Abacha a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.

Bichi ya ce ya amince da sauyin ne saboda burin sake haɗa kan jam’iyyar da kuma ƙara mata ƙarfi gabanin zaɓe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM