NE

News Elementor

Kotun Daukaka Ƙara Ta tabbatar Da Hukuncin Da Ya Hana NBC Cin Tarar Gidajen Rediyo Da Talabijin A Najeriya

Kotun daukaka kara dake Abuja ta yi fatali da karar da hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa NBC ta shigar domin kalubalantar hukuncin babbar kotun tarayya da yah ana mata cin tarar gidajen radio da television a fadin kasar nan.

Da yake zartas da hukuncinsa, mai shari’a Oyebiola Oyewumi, a madadin sauran alkalan kotun su uku, ya tabbatar da hukuncin da ya soke tarar da NBC ta ci wasu kafafen yada labarai 45 a ranar 1 ga watan Maris na 2019 saboda sabawa dokokin yada labarai na Nigeria.

A wani bayani da jami’in yada labarai na kungiyar MRA, Idowu Adewale ya fitar, ya ce hukuncin kotun na zuwa ne bayan karar da kungiyar ta shigar a watan Nuwamban 2021, inda ta kalubalanci NBC wajan cin tarar kafafen yada labarai.

A hukuncin da babbar kotun tarayya ta zartas a ranar 10 ga watan Mayin 2023, mai shari’a James Omotosho, ya amince da bukatar MRA bayan hukumar NBC ta kasa kare kanta.

Kotun ta ce ana cin tara ne kan mutanen da aka kama da laifi, kuma a karkashin dokokin Nigeria, kotuna ne kadai ke da hukuncin ayyana tara kan mutum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM