NE

News Elementor

Kotun Ƙolin Najeriya Ta Tabbatar Da Hukuncin Kisa Ga Maryam Sanda kan Kisan Mijinta, Bilyaminu.

Babbar koto a Najeriya ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda bisa samunta da laifin kashe mijinta.

Alƙalan kotun guda huɗu a cikin biyar ne suka tabbatar hukuncin, inda ake yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan watsi da ɗaukaka ƙararta, kamar yadda mai shari’a Moore Adumein ne ya sanar da hukuncin a madadin sauran alƙalan.

Kotun ta ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi rangwame ga Maryam alhalin ana ci gaba da sauraron shari’arta a gaban kotun ɗaukaka ƙara, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

A ranar 27 ga watan Janairun 2020 ne kotu a Abuja ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifin da kashe mijinta Bilyaminu Bello a gidansu da ke Abuja a shekarar 2017.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM