Najeriya da Cote d’Ivoire sun tura kimanin sojoji 200 zuwa Jamhuriyar Benin, bayan yunkurin juyin mulkin da ya faru a ranar 7 ga Disamba, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.
Ko da yake ECOWAS ba ta bayyana adadin sojojin da ta tura ba, ƙungiyar ta ce Ghana da Saliyo ma za su ba da dakaru a matsayin wani ɓangare na tsarin rundunar tsaron gaggawa da ta tanada.
Da yake jawabi a taron manema labarai a Abuja a jiya Alhamis, ministan harkokin wajen Benin, Olushegun Adjadi Bakari, ya ce a halin yanzu akwai kusan sojoji 200 da suka isa domin taimaka wa rundunar tsaron Benin a matsayin sharar fage domin wanzar da zaman lafiya.
Ya ƙara da cewa an shawo kan yunkurin juyin mulkin tun kafin neman goyon bayan ECOWAS.
A nasa ɓangaren, ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa haɗin gwiwar difilomasiyya da soji da bayanan sirri tsakanin Najeriya da Benin ne ya taimaka wajen dakile juyin mulkin.
Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje sun nuna cewa shugaban juyin mulkin, Pascal Tigri, tare da abokan aikinsa, sun tsere ne zuwa ƙasar Togo.