NE

News Elementor

Kungiyar Yiaga Africa Ta Ce Fiye Da Rabin Yan Najeriya Ba Su Gamsu Da INEC Ba,

Wata kungiya mai zaman kanta da ake kira Yiaga Africa, ta ce fiye da rabin yan Nigeria ba su gamsu da hukumar zabe ta kasa ba, INEC, saboda abubuwan da suka sha faruwa a baya.

Directan zartaswa na kungiyar, Samson Itodo ne ya bayyana hakan, a shirin Prime Time na gidan television na Arise.

Ya ce yanayin da ake samu na cin karo da juna wajan fitar da sakamkon zabe, da kuma yadda wasu jami’an ke kokarin juyar da zabin alumma, na sanyaya guiwar masu zabe a kasar nan.

A cewarsa, a bayyane take cewa fiye da rabin yan Nigeria ba su gamsu da hukumar INEC ba, kuma daya daga cikin dalilansu shi ne abubuwan da suka faru na rashin gaskiya a zabukan baya.

Itodo ya kara da cewa, halayyar sauran masu ruwa da tsaki a sha’anin zabe, musamman jami’an tsaro da bangaren shari’a, shi ma ya taimaka sosai kan yadda yan kasa ke kallon harkokin zabe a Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM