NE

News Elementor

Mai baiwa Gwamnan Kano shawara ya naɗa ɗansa a matsayin shugaban ma’aikata na ofishinsa

Mai baiwa Gwamnan Kano shawara kan yaɗa labarai, Ahmad Aruwa, ya naɗa ɗansa, Aliyu Ahmed, a matsayin Shugaban Ma’aikata (Chief of Staff) na ofishin sa.

An sanar da naɗin Aliyu tare da na wasu mutum huɗu a ranar Talata, 27 ga Oktoba, 2026.

Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Habibu Liman a matsayin Sakatare na Musamman, Adamu Mai Salati a matsayin Jami’in Protocol, Isa Ahmed Don a matsayin Darakta-Janar na yaɗa labarai da Sadarwa, da Musa Muhammad Daurawa a matsayin Mataimaki na Musamman.

Da yake jawabi bayan karɓar takardar naɗinsa, Aruwa ya sha alwashin yin aiki tuƙuru domin tabbatar da amincewar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna masa.

Ya bayyana cewa gwamnan ne jagoransa da shugabansa na siyasa, yana mai cewa zai yi duk mai yiwuwa domin ganin nasarar gwamnan a kowane mataki.

Aruwa ya kuma yaba wa tawagarsa ta yaɗa labarai bisa goyon baya da jajircewarsu, tare da bayyana kwarin gwiwar cewa za su ci gaba da aiki tare wajen yaɗa manufofi, shirye-shirye da nasarorin gwamnatin Jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM