Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada aniyarsa ta gyara da farfaɗo da matatun man fetur na ƙasa da suka daina aiki, yana mai cewa ba za a bari su zama jarin da aka zuba amma ba ya samar da amfani ba, duk da ƙaruwar ƙarfin tace mai da kamfanoni masu zaman kansu ke da shi a Najeriya.
Tinubu, wanda Sakatariyar Dindindin ta Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, Patience Oyekunle, ta wakilta, ta bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin taron makon makamashi na OTL Africa Downstream karo na 20 da aka gudanar a Legas. Ta ce gwamnati na bin sabuwar hanya mai tsauri da za ta tabbatar da cewa gyaran matatun ya kasance mai ɗorewa ta fuskar kasuwanci, tare da yin cikakken binciken fasaha, ƙarfafa haɗin gwiwa da inganta yadda ake gudanar da ayyukansu.
Matatun man Fatakwal, Warri da Kaduna, waɗanda Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPC, ke kula da su, sun daɗe ba sa aiki yadda ya kamata, duk da biliyoyin nairori da aka kashe wajen gyara su a shekarun baya. Sai dai shugabancin NNPC na yanzu ya rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da wasu kamfanonin China guda biyu domin farfaɗo da matatun.
Shugaban ƙasar ya ce manufar gwamnati ita ce Najeriya ta riƙa tace kaso mai yawa na ɗanyen man da take haƙowa a cikin gida, ta samar da ƙarin darajar tattalin arziki ga ƙasar, sannan ta zama amintacciyar mai samar da makamashi ga sauran ƙasashen Afirka.
Ya kuma bayyana cewa Najeriya na sauyawa daga tsarin da ya dogara da shigo da man fetur daga ƙasashen waje zuwa tsarin da ya fi mayar da hankali kan tace mai a cikin gida, zuba jarin kamfanoni masu zaman kansu, ingancin kasuwa da gasa a yankin Afirka.
Tinubu ya ƙara da cewa gyare-gyaren da aka gabatar ƙarƙashin Dokar Masana’antar Man Fetur ta Najeriya, wato Petroleum Industry Act (PIA), na da nufin samar da masana’antar mai mai gaskiya, mai ɗorewa ta fuskar kasuwanci kuma mai jan hankalin masu zuba jari, domin ƙara amfanar ’yan Najeriya.