
Majalisar Tarayya ta ɗage komawa zaman ta da aka shirya yi a ranar 24 ga Fabrairu, 2026.
Majalisun biyu sun ɗage zaman na tsawon makonni biyu domin bai wa kwamitocinsu damar gudanar da zaman kare kasafin kuɗin shekarar 2026 na ma’aikatu, sassa da hukumomi , da kuma hukumomin gwamnati masu zaman kansu.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, magatakardan Majalisar Tarayya, Kamoru Ogunlana, ya ce an ɗage komawar ne domin bai wa kwamitoci damar kammala zaman kare kasafin da suke yi.
Sanarwar ta ce, “An ɗage komawar ne domin bai wa kwamitocin Majalisar damar kammala zaman kare kasafin da ake yi a halin yanzu.“Yanzu za a koma zaman majalisa a duka majalisun biyu a ranar Alhamis, 5 ga Maris, 2026 da ƙarfe 11:00 na safe.
“Ana roƙon Sanatoci masu girma da kuma Ƴan Majalisar Wakilai su lura da sabon ranar da lokacin komawa zaman.“Shugabannin Majalisar na ba da haƙuri kan duk wata matsala da ɗagewar ta haifar.”