
Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu hazo da gajimare a sassa daban-daban na ƙasar nan daga ranar Litinin zuwa Laraba.
A cikin rahoton da ta fitar a Abuja, hukumar ta ce yankin Arewa zai fuskanci hazo mai sauƙi zuwa matsakaici, musamman a jihohin Borno da Yobe inda hangen nesa zai ragu zuwa kilomita 2 zuwa 5.
Haka kuma, Arewa ta Tsakiya za ta samu hazo, yayin da ake sa ran ƙura mai yawa a wasu lokuta zuwa ranar Laraba.
A yankin Kudu kuwa, NiMet ta yi hasashen yanayi mai gajimare tare da hasken rana a wasu lokuta, da yiwuwar tsawa da ruwan sama mai sauƙi a jihohin Cross River, Akwa Ibom, Legas, Ogun, Ondo, Edo, Bayelsa, Rivers da Delta.
Hukumar ta shawarci jama’a da su ɗauki matakan kariya, musamman masu fama da cututtukan numfashi kamar asma, tare da yin taka-tsantsan yayin tuƙi a lokacin ruwan sama. Ta kuma buƙaci kamfanonin jiragen sama da su riƙa samun rahoton yanayi daga NiMet domin tsara ayyukansu yadda ya kamata.