
Majalisar dattawa ta bada kariya kan amincewa da kudurin dokar yansandan jihohi, matakin ta ce na da alaka da karuwar matsalolin tsaro a kasar nan, bawai wani abu ne na siyasa ba.
A wani bayani da sashen yada labarai na ofishin jagoran majalisar, Opeyemi Bamidele ya fitar, ya bayyana kudurin a matsayin tilas bawai siyasa ba, inda ya ce sai da aka gudanar da tuntuba a fadin kasar nan gabanin ayyana kudurin.
A ranar 11 ga watan Yuni ne majalisar wakillai ta amince da kudurin na kafa yansandan jihohi, yayin da ita kuma majalisar dattawa ta amince da shi a ranar 24 ga wata, wani yunkuri da ya bawa Nigeria damar amfani da tsarin yansanda guda biyu.