NE

News Elementor

Malamai sama da 200 sun yi murabus daga aiki a jami’ar jihar Kaduna KASU

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ta ce sama da malamai 200 sun bar jami’ar sakamakon rashin kyawun yanayin aiki da kuma rashin aiwatar da yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta cimma da ASUU a shekarar 2025.

Shugaban kungiyar ASUU na jami’ar KASU, Dr Abubakar Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna.

Sakamakon haka, kungiyar takan bai wa mahukuntan jami’ar da sauran masu ruwa da tsaki wa’adin makonni biyu su fara aiwatar da yarjejeniyar tare da tabbatar da aiki da ita a jami’ar. Kungiyar ASUU ta yi gargadin cewa, idan ba a dauki matakin da ya dace ba, za ta tsunduma yajin aiki na gaba daya kuma na sai baba-ta-gani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM