Kotun Maroko da ke birnin Rabat ta yanke wa magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Senegal hukuncin dauri daga watanni uku zuwa 12.
Magoya bayan kungiyar dai na tsare a Maroko tun bayan kammala gasar karshe da aka yi a ranar 18 ga watan Janairu, wanda Senegal ta lallasa Moroko da ci 1-0. Maroko dai ta zargi magoya bayan Senegal da tada zaune tsaye da kuma harkar daba a yayin gasar cin kofin nahiyar Afrika AFCON.
Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Senegal, Bacary Cisse, ya nuna takaicinsa kan wannan hukunci mai tsauri kan magoya bayan kungiyar, kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
An dai yanke wa mutum Tara hukuncin daurin shekara guda da tarar dirhami 5,000 kwatankwacin dalar Amurka $545, sai kuma wasu mutum shida da aka yanke wa hukuncin daurin watanni shida da tarar dirhami 2,000, sai kuma wasu mutum biyu da aka zartar musu da hukuncin daurin watanni uku da kuma tara ta dirmani 1,000.