NE

News Elementor

Matawalle Ya Maganta Kan Zarginsa Da Alaƙa Da Ƴanbindiga

Ƙaramin ministan tsaron Najeria Bello Matawalle da ƙasurgumin ɗan bindigar nan Bello Turji, sun mayar da martani kan ce-ce-ku-cen da ake ci gaba da yi game da zargin ministan da alaka a ‘yan bindiga lokacin da yake gwamnan Zamfara.

Cikin wani faifan bidiyo, Bello Turji ya musanta ikirarin cewa ya karɓi kuɗi daga Bello Matawalle sai dai ya amsa cewa ya taɓa haɗuwa da gwamnan a wancan lokaci a fadar gwamnati yayin tattaunawar zaman lafiya.

A cikin wata hira da aka yi dashi, Matawalle ya amince cewa an aikawa yan bindiga wasu abubuwa amma a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar zaman lafiyar da suka cimma ne.

Waɗannan maganganu dai sun tayar da ƙura a Najeriya saboda yadda wasu ke zargin tsohon gwamnan na Zamfara da hannu wajen marawa ƴanbindiga baya amma a tattaunawar da suka yi a kafan yaɗa labarai ta intanet ta DCL Hausa, ya musanta waɗannan zarge-zarge.

“Shi zargi wanda ba a tabbatar da shi a kotu ba ba zama gaskiya ba, duk wani me zargi na ya je kotu, amma da sharaɗi, idan aka tabbatar da duk abin da ya fadi ba gaskiya bane a kai, toh duk abin da na aza mai na damaiji dole sai ya biya,> in the ƙaramin ministan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM