NE

News Elementor

Ministan lafiya ya ce an mayar da matar da ta kamu da Ebola a Najeriya zuwa ƙasarta Switzerland

Ministan Lafiya na Najeriya, Ali Pate, ya bayyana cewa an kwashe mara lafiyar farko da aka tabbatar ta kamu da cutar Ebola da aka shigo da ita Najeriya zuwa ƙasar Switzerland domin ci gaba da ba ta kulawar lafiya.

Pate ya bayyana cewa an tashi da mara lafiyar daga Abuja a safiyar Litinin da amincewarsa, inda ya ƙara da cewa mijinta, wanda har yanzu bai nuna alamun cutar ba, ya raka ta.

A cikin wata sanarwa, ministan ya ce yanayin lafiyar mara lafiyar ya ƙara inganta kafin a kwashe ta zuwa Switzerland.

Ya ce lafiyarta ta daidaita kuma tana cikin hayyacinta, sannan tana iya magana, yayin da sakamakon gwaje-gwajen da aka yi mata a dakin gwaje-gwaje ya kusa komawa yadda yake a matakin da aka saba gani.

Sai dai Pate ya yi gargaɗin cewa samun sauƙin da mara lafiyar ta yi ba yana nufin cewa ta daina iya yaɗa cutar ba, inda ya jaddada cewa ana ci gaba da bin tsauraran matakan kare lafiyar jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM