Fitaccen jarumin masana’antar Kannywood, ya tabbatar da rabuwa da matarsa Maimuna Musa, wadda aka fi sani da Maimuna Pretty.
A wani rubuta da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, jarumin ya ce jininsu ne suka gano ya zo ɗaya, shi ya sa suka amince su rabu.
“Da gaske mun rabu da matata saboda mun gano muna da jini iri ɗaya. Ita AS ce nima AS ne. Don haka kada a mayar da wannan al’amarin namu ya zama wata maganar daban, ko kuma a riƙa yaɗa ƙarya,” in ji shi.
Zango ya ƙara da cewa ya yi wannan rubutun ne domin ya yi wa magoya bayansa cikakken bayanin abin da ke faruwa.
Ya wallafa wani faifan bidiyo a ƙasan rubutun, inda ya ƙara da cewa, “za ku iya gani wannan bidiyon an naɗe shi ne a jiya da take barin gidana cikin nishaɗi.”