Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaduwa ta (NCDC) ta bayyana cewa cutar zazzabin Lassa ta yi sanadin mutuwar mutane 214 a faɗin ƙasar nan tun daga farkon shekarar 2026.
A cewar rahoton mako na 23 na hukumar, adadin mace-macen ya kai kashi 25 cikin 100, idan aka kwatanta da kashi 18.9 cikin 100 a daidai wannan lokaci a shekarar 2025.
NCDC ta ce adadin waɗanda ake zargi da kamuwa da cutar da kuma waɗanda aka tabbatar sun kamu ya ƙaru idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Rahoton ya nuna cewa an samu sababbin masu cutar a jihohin Edo, Ondo, Bauchi da Ebonyi a mako na 23, yayin da ba a samu sabon ma’aikacin lafiya da ya kamu da cutar ba.
Hukumar ta bayyana cewa cutar ta bazu zuwa jihohi 23 da ƙananan hukumomi 109 tun daga watan Janairun 2026.
Jihohin Ondo, Bauchi, Taraba, Edo da Benue ne suka fi yawan masu cutar, inda suka kai kashi 84 cikin 100 na dukkanin mutanen da aka tabbatar sun kamu.
NCDC ta kuma ce matasa masu shekaru tsakanin 21 zuwa 30 ne suka fi kamuwa da cutar, yayin da shekarun masu cutar suka kama daga shekara ɗaya zuwa shekaru 93.
Hukumar ta ce tana ci gaba da gudanar da ayyukan sa ido da kula da masu cutar a jihohin da abin ya shafa, tare da haɗin gwiwar hukumomi da abokan hulɗa domin dakile yaɗuwar cutar.